Kura Ta Fara Lafawa A Bwari Dake Dab Da Abuja

Shagunan da aka kona a rikicin garin Bwari dake kusa da Abuja

Yanzu dai zaman lafiya na kankama a garin Bwari dake yankin babban birnin tarayyar Najeriya biyo bayan rikicin da yayi sanadiyyar kone babbar kasuwar garin da ma karin wasu gine gine da wuraren hada hadar kasuwanci.

Wakilinmu Hassan Maina kaina da yanzu haka yake garin ya ga dimbin jami'an tsaro na sojoji da 'yan sanda cikin damara su na ta sintiri ba kakkautawa.

Da yake tattaunawa da VOA Hausa, Mai Martaba Sarkin Bwari, Alhaji Auwal Muhammad Musa Ijakoro, ya ja hankalin jama'a kan muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin jama'a, yana mai kiran da a yi taka tsantsan, a kuma daina daukar doka a hannu.

Wasu daga cikin jama'ar garin da suka tattauna da Muryar Amurka sun nemi ma'aikatar raya babban birnin tarayya ta tallafawa wadanda suka yi hasarar dukiyoyi sanadiyyar wannan rikici, yayin da wasu kuma suka nemi a hukumta duk wanda aka samu da hannu ko taka rawa wajen haddasa rikicin.

Your browser doesn’t support HTML5

Kura Ta Fara Lafawa A Bwari