Kurdawan Syria Sun Dauki Matakan Tafiyar Da Harkokin Arewa Maso Gabashin Syria

Da taimakon Amurka, a makon da ya gabata kungiyoyin Kurdawa na Syria suka sanar da daukar matakin farko a kokarin tafiyar da harkokin arewa maso gabashin Syria.

Tun daga shekarar 2012, yankin da galibinsa Kurdawa ne ke karkashin ikon ‘yan kungiyar YPG da bangarenta a fagen siyasa, wato jam’iyyar PYD. ‘Yan YPG su ne suka fi yawa a rundunar dakarun SDF da Amurka ke mara wa baya.

Dakarun SDF sun kasance kawaye da Amurka a yakin da su ke yi da mayakan IS a Syria.

Bayan wadannan kungiyoyin, kungiyar kurdawa ta ENKS da ke Syria ita ma wata kungiya ce da ta kunshi jam’iyyun siyasa da yawa. Kungiyar ta ENKS ta nuna rashin amincewarta da kungiyar PYD da kuma gwamtinta a arewa maso gabashin Syria.

Jami’an Amurka na fatan bangarorin biyu za su kawar da bambance-bambancensu, su maida hankali akan inganta shugabancin yankin, a kasar da yaki ya daidaita.