Kwamishanan 'Yansandan Jihar Oyo Ya Yi Taron Inganta Tsaro

Solomon Arase, babban sifeton 'yansandan Najeriya

Sabon kwamishanan 'yansandan jihar Oyo Mr. Leye Oyebade ya yi taro da masu ruwa da tsaki saboda inganta harkokin tsaro a jihar.

Wadanda kwamishanan ya tara wurin taron sun hada da kungiyar 'yan sintiri da sarakunan gargajiya da kungiyar dalibai da kungiyar mata da shugabannin addinai da masu gidajen otel otel saboda lalubo hanyar samarda ingantacen tsaro ga jama'ar jihar.

Kwamishana Oyebade yace matakin da suka dauka yana cikin shirin babban sifeton 'yansandan Najeriya Mr. Solomon Arase na samarda zaman lafiya tsakanin al'umma.

Kwamishanan yace dole ya jaddada cewa 'yansanda ashirye suke su samarda tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a. Saboda haka ya bukaci jama'a da su hada kai da 'yansanda tare da baiwa 'yansandan bayanai masu ma'ana domin a gano masu aikata laifuka.

Wasu da suka halarci taron sun fadi albarkacin bakinsu. Suna ganin an fara da kafar dama idan kuma aka cigaba haka za'a sami nasara.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwamishanan 'Yansandan Jihar Oyo Ya Yi Taron Inganta Tsaro