Kwamitin Majalisar Wakilan Amurka Na Kan Kammala Rahoton Yiwuwar Tsige Trump

Kwamitin Majalisar Wakilan Amurka Kan Bayanan Sirri Na Shirrin Sakin Rahoton Yiyuwar Tsige Trump.

Ana kyautata zaton Kwamitin Majalisar Wakilan Amurka kan bayanan sirri, yau dinnan Talata, zai gabatar ma jama'a sakamakon bincikensa da kuma matakan da ya bayar da shawarar a dauka a binciken yiwuwar tsige Shugaban Amurka Donald Trump.

Shugaban Kwamitin, Adam Schiff ya fada wa kafar labarai ta MSNBC a daren jiya Litinin cewa, kwamitin na kan kammala rahoton. Ya kuma ce kwamitin zai kada kuri'a da daren yau Talata kan batun mika rahoton a hukumance ga kwamitin shari'a, wanda mambobinsa za su yanke shawara kan ko za su rubuta takardar bukatar tsige Shugaba Trump ko a'a.

Kwamitin Shari’a na shirin fara nasa zaman sauraren ba'asin ranar Laraba, kuma za su yi hakan ba tare da lauyan Trump ya na wurin ba.

Shugaban ya ce ba zai tura wakilai ba "saboda gaba daya rudani ne."