Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya Ya Jefa Kuri'a Kan Wa'adin Tsaron A Afirka Ta Tsakiya

Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ya jefa kuri'ar bai daya ta amincewan kan kara wa'adin ayyukan kwamitin a aikin samar da zaman lafiya a kasar Africa ta Tsakiya har zuwa watan Nuwambar shekarar 2017 , makonni kadan bayan da Faransa ta fitar da sanarwar kaswhe sojojin ta a kasar.

A jiya Talata ne dai Kwamitin tsaron ya kaddamar da wannan kudurin wanda yayi wa lakabi da MINUSCA, wanda zai kai har zuwa 15 ga watan Nuwambar 2017. Ya kuma nuna goyon baya ga sabon shugaban kasar Afirka ta tsakiya Faustin-Archange Touadera, wanda ya hau kujerar mulki cikin watan Maris.

Majalisar dinkin duniya dai na da yawan sojojin kiyaye zaman lafiya kusan 11,000 wadanda ke aikin kare fararen hula, suna kuma lura da kiyaye hakkin bil'adama da kuma bayar da damar shigar da kayan jin ‘kai a kasar.

‘Yan tawaye dai sun hambarar da shugaban kasar Afirka ta tsakiya cikin shekara ta 2013, inda hakan yayi sanadiyar tashe tashen hankula a kasar, lamarin da yasa Kasar Faransa ta aike sda sojojin ta a cikin watan disanba domin su agaza, sai dai yanzu haka ana sa ran sojojin ta 350 da suka rage zasu bar kasar zuwa watan Oktobar wannan shekarar.

Majalisar dinkin duniya ta fara aikawa da sojojinta a watan Afrilun 2014, biyo bayan sojojin kungiyar tarayyar Afirka domin taimakawa kare fararen hula da sauwaka shigar da kayan jin ‘kai.

A jiya Talata ne kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yace, ana samun ci gaba a harkokin tsaron kasar, amma dole aci gaba ido aka saboda barazar tashe-tashen hankulan daake samu nan da can..