Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutumin da Ya Tada Bam A Jamus Ya Taba Samun Tabin Kai


Jami'an tsaron kasar Jamus a wurin da bam din ya tashi

Jami'an kasar Jamus sun tabbatar cewa mutumin da ya tada bam a Jamus dan asalin kasar Syria ne mai shekari 27 wanda yake neman mafaka a kasar, ya taba samun tabin kai

Jami’ai a Jamus, sun ce dan kasar Syria nan mai shekaru 27 da ke neman mafaka a Jamus, wanda ya ta da bam din da ya halaka kansa kana ya raunata wasu da dama a garin Bavarian, ya taba yunkurin kashe kansa har sau biyu, ya kuma taba zuwa asibitn masu tabin hankali domin karbar magani.

Mutane uku ne suka samu munanan raunuka a harin, wanda mutumin ya kai a jiya Lahadi, bayan da aka hana shi shiga wajen wani bikin mawaka a Ansbach da ke kusa da birnin Nurmberg.

Fiye da mutane dubu biyu aka kwashe a filin wasan bayan da aka kai harin.

A bara ne aka hana maharin damar samun mafaka, amma aka bashi izinin zama a kasar ta Jamus na dan wani lokaci saboda yakin da kasarsa ta Syria ke fama da shi.

Ministan harkokin cikin gidan Jamus, Tobias Plate, ya ce ana shirin maida maharin zuwa kasar Bulgaria, amma har ya zuwa aukuwar wannan lamari ba a tantance yaushe ake shirya fitar da shi daga kasar ba.

XS
SM
MD
LG