Kwanaki Kadan Suka Ragewa Kungiyar Boko Haram A Duniya

Babban Hafsan Mayakan Saman Najeriya. Air Marshall Sadique Abubakar

Rundunar sojojin Najeriya na cigaba da kakkabe burbushin 'yan ta'addar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar sojojin saman Najeriya tace zataci gaba da fatattakar mayakan Boko Haram har sai an kawo karshensu.

Da yake jawabi ga mayakan a birnin Maiduguri, Babban Hafsan Hafsoshin rundunar sojojin saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar, yace ko kadan hadarin jirgin yakin su samfurin Mi35m da ya auku kwanan nan a Damasak ba zai sanyaya masu gwiwa ba.

Yace yanzu suna cikin yaki ne kuma kamar sauran al'amuran rayuwa shima na da nasa hadurran, Amma wannan ba zai zama wani abun da ka iya kawo cikas a kokarin gamawa da burbushin mayakan.

Yanzu haka ma dai rundunar ta tabbatar da jiragen yakin su samfurin Mi35m, da Alpha Jets da ma sauran jiragen yakinsu yanzu haka suna can suna ta barin wuta a Arewa maso gabashin Najeriya.

Masana tsaro irinsu Wing Commander Musa Isa Salmanu wanda ya jinjinawa kokarin mayakan saman ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kara samarwa mayakan saman jiragen yaki.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina daga birnin Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwanaki Kadan Suka Ragewa Kungiyar Boko Haram A Duniya 2'15"