Ma’aikata Sun Dawo Bakin Aiki Bayan Yaji

Jami'an 'yan sanda sun tsaya kuwa da sakateriyar gwamnatin tarayya a Abuja

An dawo bakin aiki a wasu sassan da suka baiwa kungiyar kwadago hadin kai, ciki harda jami’ar Abuja wadda tayi barazanar ba zata biya albashi ba matukar ma’aikatan suka ci gaba da yajin aiki.

Duk da yake zaiyi wuya a gane anyi yajin aiki a Abuja, idan aka dauke kungiyar kwadagon da tayi zanga zanga. Bawai ma’aikatan sunyi shakkar ko za a hanasu albashi bane ya hanasu shiga yajin aikin ba, rashin amincewa da nasarar da yajin zai haifarwa kasar.

Shin mai zai hana uwar kungiyar kwadagon kasar ta tara sauran kungiyoyin da suka bijire mata don asasanta kungiyar ta dawo da tasirinta kamar da. Yanzu dai kungiyar zata ci gaba da tattaunawa da gwamnati kan lumuran da suka shafi walwalar ma’aikata kamar yadda ma’ajin kungiyar Kwamared Ibrahim Khalil, ya bayyana.

Wannan dai shine karo na farko da yajin aiki a Najeriya baiyi tasiri ba, duk kuma da wannan lokaci ne aka samu karin farashin Man Fetur mafi yawa a tarihi tun ma zamanin mulkin soja.

Your browser doesn’t support HTML5

Ma’aikata Sun Dawo Bakin Aiki Bayan Yaji - 2'28"