Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Tsige Ali Modu Ta Zabi Makarfi


Sanata Ali Modu Sheriff

Rahotanni daga Najeriya na cewa babbar jam’iyar adawa ta PDP kasar ta zabi tsohon gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi a matsayin shugabanta na rikon kwarya.

A yau ne jam’iyar ya kamata ta gudanar da taron ta na gangami a birnin Fatakwal da ke jihar Rivers, amma shugabanta Sanata Ali Modu Sherrif ya dage taron, yana mai cewa kotu ta haramta gudanar da shi lura da cewa akwai wadanda suka shigar da kara suna kalubalantar shugabancinsa.

Amma rahotanni sun ce wasu daga cikin jiga jigan jam'iyar sun gudanar da taron duk da sanarwar da Sherrif ya yi, inda suka tsige shi bayan da suka rusa kwamitin zartarwar jam'iyar.

An dai zabi Sanata Makarfi ne a birnin na Fatakwal bayan da aka tsige Sherrif, wanda ya ke shirin sake tsayawa neman takarar shugabancin jam’iyar.

Wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El Hikaya da ke Abuja ya tabbatar da zabin da akawa Sanata Makarfi kamar yadda za ku ji a wannan rahoto da ya aiko mana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG