Macron Ya Sha Alwashin Sake Gina Mujami'ar Notre Dame Cikin Shekaru Biyar

Shugaban Faransa ya yi alkawarin sake gina Cocin nan mai dumbin tarihi da ke Paris a cikin shekaru biyar masu zuwa, ya kuma fadi hakan ne ta gidan talabijin din kasar a lokacin da yake wa mutan kasar jawabi.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi alkawarin sake gina Mujami’ar Notre Dame cikin shekaru biyar, bayan da gobara ta lalata cocin mai daddaden tarihi, wacce ke Paris, babban birnin kasar.

Shugaba Macron ya bayyana hakan ne, yayin wani jawabi da ya yi wa ‘yan kasar ta talbijin, dangane da wannan ibtila’i da ya abkawa Mujami’ar mai shekaru 850.

Sannan ya kara da cewa za a kayata ginin, yana kuma mai kira ga daukacin Faransawa, da su dauki lamarin a matsayin wata dama da za su dunkule wuri guda.

Ko da yake gobarar ta lashe daukacin bangaren da aka gina da katako, amma hukumomi sun ce, ma’aikatan kashe gobara, sun yi nasarar ceto fitattun hasumiyoyin Cocin guda biyu.