Mahukuntan Amurka Sun Samu Bayanan Inda Rahami Ya Say Kayan Hada Bam

Ahmad Khan Rahami wanda ya dana bam a wurare ukku a nan Amurka

Masu gudanar da bincike a Amurka, sun ce mutumin da ake zargi da kai harin bam a New York da New Jersey, ya sayo wasu kayayyakin ta da bam a kafar saye da sayarwa ta ebay, da kuma wata wayar da ya sayo a wani kanti mai nisan mita 500 daga gidansa.

Wadannan bayanai sun fito fili ne a takardun korafin da aka gabatar jiya Talata, wanda hakan zai sa a tuhumi Ahmad Khan Ramani mai shekaru 28.

Mafi yawan wadannan tuhume-tuhumen, akan yanke hukuncin daurin zaman gida yari ne har na tsawon iya rayuwa.

A ranar Litinin aka cafke Ramani, bayan da aka yi wata musayar wuta, lamarin da ya sa ya ji rauni tare da wasu ‘yan sanda biyu.

Kamar yadda wasu takardun kotu suka nuna, masu bincike sun yi amannar, cewa Ramani ya sayo wani ruwan sanadari na Acid ta hanyar yin amfani da kafar ebay, inda ya sakaya sunansa a matsayin “ahmad Rahimi, hade da wasu wayoyi da sauran kayayyakin da ke haddasa fashewa, a tsakanin ranakun 20 ga watan Yuni da ranar 10 ga watan Agusta.

A kuma ranar 12 ga watan Satumba, kayayyakin na Ramani suka isa gareshi.