Majalisa Na Shirin Kada Kuri'ar Hana Trump Kai Hari a Iran

Shugaban Amurka Donald Trump

A yau Alhamis ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta amince da wani kuduri da zai umarci shugaba Donald Trump da kada ya yi amfani da karfin soji akan Iran.

Nancy Pelosi Kakakin Majalisar Wakilan Amuirka

Kakakin Majalisar Wakilai ta Amurka, Nancy Pelosi ta sanar da kada kuri’ar da za a yi, a wata sanarwa da ta caccaki gwamnatin shugaba Trump na kai harin sama a makon da ya gabata.

Harin ya halaka kwamandan dakarun juyin juya halin Iran, Qassem Soleimani, inda majalisar ta yi korafin cewa ba a tuntube ta ba.

Pelosi ta kwatanta harin na sama a matsayin “takalar fada” wanda ka iya jefa rayukan dakaru da jami’an diplomasiyyar Amurka cikin hadari.

Sanata Chris Van Hollen Dan Majalisar Dattawan Amurka

Chris Van Hollen, Sanata a Majalisar Dattawan Amurka na bangaren ‘yan Democrat, wanda ke wakiltar jihar Maryland, ya ce, “ni a iya tawa fahimtar, sun gaza gabatar mana da kwararan hujjojin da ke nuna cewa, wani na shirin kitsa wasu hare-hare akan dakarun Amurka da Amurkawa da yawa".

Lura da cewa ‘yan Democrat ne ke da rinjaye a majalisar wakilan, ana sa ran za ta amince da wannan kuduri.

Sai dai ba a san yadda batun zai kaya a Majalisar Dattawa ba, inda ‘yan Republican ke da rinjaye.