Majalisar Dinkin Duniya Ta Ceto Wasu 'Yan Gudun Hijira a Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta kwashe ‘yan gudun hijirar Libya kusan 325 daga wata cibiyar gwamnati a Tripoli, bayan da aka yi zargin cewa, an musgunawa wasu sabili da nuna rashin gamsuwa da irin yanayin da suke zama ciki.

Fada tsakanin bangarorin dake iko a Libya ya haddasa rashin kwanciyar hankali ga fararen hula a babban birnin kasar da yankunan birnin.

“Hadarin da ‘yan gudun hijira da bakin haure ke ciki ya tsananta a yanzu” a cewar mataimakin shugaban MDD dake aikin jinkai a Libya, Matthew Brook, ya fadi jiya Laraba cewa “Yana da muhimmanci a kyale ‘yan gudun hijiran dake cikin hadari su fice zuwa inda zasusami kwanciyar hankali.”

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta ce, matsayar da ta dauka ta kwashe ‘yan gudun hijirar Qaser Ben Gasheer a Tripoli, ya faru ne dalilin wani rahoton dake cewa ana dukan wasu tare da yi musu barazana da harbin bindiga, saboda suna kukan halin da suke ciki kan rashin abinci.

An kai mutane 12 Asibiti .