Majalisar Dinkin Duniya ta dage takunkumin da ta kakabawa Ivory Coast

Ban Ki-moon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Jiya Alhamis kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ya dage takunkumin shekaru goma sha biyu na hana sayarwa kasar Ivory Coast makamai

Kwamitin sulhun ya kuma sabunta aikin kiyaye zaman lafiya da Majalisar ke yi a kasar na tsawon shekara daya.

Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa kasar takunkumin ne a shekarar dubu biyu da hudu bayan yakin basasar da aka yi a kasar daga shekara ta dubu biyu da biyu zuwa shekara ta dubu biyu da uku.

Kudurin da aka amince dashi bai daya a kwamitin , ya kuma yi maraba da shawarwarin da ake yi tsakanin jam'iyyun siyasar kasar da kuma ingantuwar kare hakki da 'yancin jama'a a kasar.

Yanzu haka akwai sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dubu shida da dari tara a kasar ta Ivory Coast.

To sai dai jam'iyyun masu hamayya da kungiyoyin kare hakkin jama'a a kasar sun yi Allah wadai da kudurin na Majalisar Dinkin Duniya.

Babban sakataren MDD a tsakiya yayinda suke taro