Majalisar Dinkin Duniya Ta Tabbatar Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Yamal

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a kan batun Yamal

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya(MDD) bai daya ya tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin birni Hodeida mai tsahar jirgin ruwa kuma birnin mai muhimmanci a Yamal.

An cimma wannan yarjejeniya ce a wata tattunawa tsakanin bangarori masu gaba da juna a Yamal da MDD ta jagoranci a makon da ya gabata a babban birnin kasar Sweden.

Kudurin ya amince da duk wata yarjejeniyar da bangarorin suka cimma a birnin Stockholm, inji jakadiyar Birtaniya a kan kwamitin Karen Pierce da tawagarta da shirya daftarin. Muhimman abubuwa dake kunshe a cikin yarjejeniyar sun hada da tsagaita wuta, da kuma janye sojoji a birnin Hodeida kuma hakan ya fara daga ranar 18 ga watan Disemba. Kudurin ya kuma umarci MDD ta taimaka wurin aiwatar da yarjejeniyar da kuma sa ido a kan batun.

MDD zata sa ido a kan tsagaita wuta kuma kamar yanda kudurin ya bata umarni, zata fara tura tawagarta ta farko a kan wannan batu da zasu kwashe tsawon kwanaki talatin a wurin, karkashin jagorancin tsohon kwandan rundunar kwantar da tarzoma ta MDD kuma dan kasar Netherlands General Patrick Cammaert kuma tuni an riga an tura shi yankin.