Majalisar Dinkin Duniya Ta Zabi Mutane 25 Su Jagoranci Magance Tamowa

Scaling Up Nutrition

Rahoton da wata kungiya dake taimakawa kan muhimmancin abinci mai gina jiki, mai suna "Scaling up Nutrition" ta fitar, ya bayyana cewa mutum guda cikin mutane uku a fadin duniya na fama da tamowa ko rashin abinci mai gina jiki.

Kan haka Majalisar Dinkin Duniya ta zabi Aliko Dangote, da shugaban bankin raya Afirka, da wassu mutane 25 a fadin duniya su jagoranci magance matsalar tamowa, kafin shekara 2030.

Duk da kokarin da hukumomi ke yi na dakile matsalar tamowa, bayanai na nuni da cewa akwai dimbin masu fama da lalurar, musamman a yankunan da aka sami yake-yake.

A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dinkin Duniya Ta Zabi Mutum 25 Su Jagoranci Magance Tamowa