Makamai sun Taimaka Wajen Samun Nasarorin Sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya (File Photo)

An danganta nasarorin da dakarun sojojin Najeriya, ke samu kan ‘yan kungiyar Boko Haram, ga samarda isassun makamai

An danganta nasarorin da dakarun sojojin Najeriya, ke samu kan ‘yan kungiyar Boko Haram, ga samarda isassun makamai da kuma taimakon jama’ar yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban hukumar ware da kan jama’a ta gwamnatin tarayya Mr. Mike Omeri, ne ya furta haka a wata hira da suka yi da wakilin mu Ibrahim Garba ta wayar tarho.

Ya kara da cewa kasashen dake makwabtaka da Najeriya, suma sun taka rawar gani wajen nasarorin da Sojojin suka samu.

Mr. Omeri, ya jadada cewa har yanzu ana samu ‘yan kungiyar ta Boko Haram da suke mika kansu ga hukumomi don kansu.

Your browser doesn’t support HTML5

Nasarorin Sojojin Najeriya - 2'41"