Manoman Auduga Sun Samu Tallafi a Jihar Pilato

Manoma.

Manoman auduga fiye da 5,000 a jihar Pilato sun amfana daga shirin nan na "Anchor Borrower Scheme," ta hanyar samun angurya, taki da magungunan feshi.

Da take kaddamar da shirin, jami’ar babban bankin Najeriya, reshen jihar Pilato, Madam HelenTemtsen ta ce kananan hukumomi biyar ne za su ci amfanin shirin a jihar, da suka hada da Kanke, Kanam, Wase, Langtang ta Kudu da Bassa.

Wasu da suka amfana da shirin sun bayyana farin cikinsu da cewa za su sami ingancin rayuwa a fannin noman auduga.

Jami’in ma’aikatar inganta ayyukan noma a Pilato, Luka Kefas, ya ce farfado da noman auduga zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Madam Tabitha Apolos ta ce samar da auduga a Najeriya zai rage irin atamfofin roba marasa inganci da ke kasuwanni.

Shugaban kungiyar manoman auduga a jihar Pilato, Mohammad Garba Garga, ya ce gwamnati ce za ta sayi audugar daga manoman.

Domin karin bayani, saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Jos

Your browser doesn’t support HTML5

Manoman Auduga Sun Samu Tallafi a Jihar Pilato"