Manoman Shinkafa A Najeriya Sun Koka Da Matakin Gwamnati

Manoman Shinkafa

Manoman shinkafa sun fusata game da baiwa wasu kamfanoni izinin shigowa da shinkafa Najeriya baya ga ta gida

Kasancewar jihar Adamawa, cibiyar noman shinkafa kamar jihar Kebbi, manoman shinkafa a jihar sun koka akan labarin cewa gwamnati ta bada izinin a shigo da shinkafar kasar waje, bayan alkawurra a baya na cewa baza a sake barin a shigo da shinkafar kasar waje cikin Najeriya ba, bayan kuma sun noma nasu sun kai kasuwa.

Lake Rice dai ita ce shinkafar da gwamnati ke tinkaho da ita, ana noma ta ne a jihar Kebbi mai rafin ban ruwa da yawa, da hadin guiwar jihohin Legas da Kebbi wanda gwamnatin tarayya ta tallafawa ya ba manoma damar noma shinkafa mai daukar ido da nagarta. Sai dai kuma jin cewa an baiwa wasu kamfanoni uku damar kawo shinkafa ta jirgin ruwa, yasa manoman shinkafa harzuka inda suka fita zuwa fadar gwamnati dake Yola don kai kokensu.

Mr Steven Madwa shugaban hadakar kungiyar manoman shinkafa a jihar Adamawa wanda shi ya jagoranci wannan zanga-zangar zuwa gidan gwamnati inda suka mika takardar kokensu, yace suna goyon bayan gwamnatin tarayya na inganta harkokin noma a kasar to amma basu yarda da shigo da shinkafa yar waje ba.

Kungiyar manoman na zargin cewa wasu kusoshin gwamnatin kasar ne ke neman kawo sauyi a matakin da tun farko shugaba Buhari ya dauka na hana shigo da shinkafa yar waje.

Da yake karbar takardar koken a madadain gwamnan sakataren gwamnatin jihar Dr Umar Bindir yace sun kawo kukansu inda ya dace, kuma mun yi alkawarin za a mika wannan kukanku ga mukaddashin shugaban kasa ba da wani jinkira ba.

Bunkasa harkar noma,musamman na shinkafa na cikin kudurorin gwamnatin APC wanda hakan yasa gwamnati da kuma manoma zabura domin bunkasa wannan harka,koda yake wasu na ganin akwai sauran rina a kaba.

Your browser doesn’t support HTML5

Manoman Shinkafa A Najeriya Sun Koka Da Matakin Gwamnati - 2'56"