Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Kasar Phillipines Sun Shiga Birnin Marawi A Tsibirin Mindanao.


Sojojin Gwamnatin Phillipines Yayin Da Suke Fafatawa Da 'Yan Tsageru.
Sojojin Gwamnatin Phillipines Yayin Da Suke Fafatawa Da 'Yan Tsageru.

Kasar Phillipines tayi kokarin kakkabe Tsageru masu Kishin Islama a Birnin Marawi.

Dakarun kasar Phillipines sun shiga wani birni mai fama da fitina a tsibirin Mindanao na kudancin kasar a yau Alhamis, a wani yunkurin kakkabe tsagera ‘yan kishin Islama da suka kama birnin a farkon makon nan.

Jiragen saman yaki masu saukar ungulu guda biyu sun yi shawagi a samaniyar birnin yayin da wasu tankoki masu sulke suka kutsa cikin unguwanninsa, ana harbe-harbe da fashe-fashe. Yanzu haka dai yawancin mutane dubu 200 dake zaune cikin birnin na Marawi suna arcewa domin ceton rayukansu.

Wannan rikicin dai ya fara ne da maraicen ranar Talata a lokacin da jami’an tsaron Phillipines suka kaddamar da shirin kama wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Isnilon Hapilon, wanda ake kyautata zaton yana cikin Marawi ana yi masa jinyar raunukan da ya samu a wani fada da aka yi a baya. Samamen bai yi nasara ba bayan da wasu ‘yan bindiga suka afkawa birnin suna kona gidaje, da wata jami’a, da majami’un katolika, tare da sace mutane, ciki harda wani shugaban wata majami’a da kuma wasu ‘yan majami’ar su fiye 10.

Rundunar sojan kasar ta ce an kashe akalla sojojin gwamnati guda 6, ‘yan bindiga 13 kuma sun rasa rayukansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG