Masarautun Jihar Nasarawa Sun Dauki Matakan Samar Da Zaman Lafiya

Masarautar Keana a jihar Nasarawa tace matakan da ta dauka na hada kan dukkan kabilu da al’umman yankin sun taimaka wajen samar da zaman lafiya matuka.

Mai martaba Osana na Keana, Alhaji Abdullahi Amegwa Abgo na uku, yace sun yi nazari, kan dalilan dake haddasa sabani tsakanin al’umman yankin, suka kuma magance su.

Shugaban karamar hukumar Keana, Adamu Adi Giza yace zaman tattaunawa, da fahimtar juna, ya taimaka sosai wajen dinke barakar dake tsakainsu.

A saurari cikakken rahoto daga wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Masarautar Jihar Nasarawa Sun Dauki Matakan Samadda Zaman Lafiya