Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Mahaifiyar Wani Dan Majalisar Nijar

Ginin majalisar dokokin kasa a Yamai, babban birnin Nijar

A jamhuriyar Nijar wasu ‘yan bindiga sun sace mahaifyar wani dan Majalisar Dokoki a kauyen Gueskerou dake yankin Diffa, suna neman a biya su kudin fansa.

Wannan lamari na zuwa ne kwana guda bayan da masu garkuwar suka saki wani ‘dan kasuwa dake hannunsu bayan da ya biya Miliyan 20 na kudin CFA.

Rahotanni sun nuna cewa da missalin karfe 10 na daren ranar Litnin ne ‘yan bindigar suka yi awon gaba da mahaifiyar dan Majalisar Dokokin Nijar mai wakiltar yankin Diffa, Boulou Mahamadou. Sa’o’i kadan bayan da suka saki dan kasuwa, Kaka Touda Goni mamadou, wanda ya fanshi kansa ta hanyar biyan makudan kudade.

Har ya zuwa hada wannan rahotan ‘yan bindigar na ci gaba da garkuwa da wannan mata, yayin da wata majiya ke cewa an fara tattaunawa domin shawo kan wannan al’amari cikin ruwan sanyi.

Ya zuwa yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin garkuwar da ake da mutane.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Mahaifiyar Wani Dan Majalisar Nijar - 2'35"