Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libiya Ta Cimma Tsagaita Wuta, Amma Wuta Na Tashi


 Ahmed Maiteeq
Ahmed Maiteeq

Bayan labari mai dadi na cimma jituwa tsakanin bangarorin da ke yaki a Libiya, wadanda har su ka yi alkawarin kwance damara, sai kawai aka ji barin wuta da cikin dare a birnin Trabulus (Tripoli). Amma har yanzu ana sa ran dorewar yarjajjeniyar.

Kafafen yada labarai na kasashen Larabawa sun ba da rahoton cewa bangarorin da ke yaki da juna a Libiya sun amince su tsagaita wuta, to amma babu tabbacin dorewar yarjajjeniyar. Tuni ma aka samu rahoton fafatawa da dare a birnin, kuma an rufe filin jirgin sama daya tilo da ke aiki a birnin Tripoli bayan da rokoki su ka dira wajen ranar Jumma’a.

Kungiyoyin mayaka daga bangarori dabam-dabam sun yi ta barin wuta a sararin sama daura da sansanin soji na Yarmouk, inda aka ja daga cikin ‘yan kwanakin nan. Sansanin sojin ya fada hannun bangarori dabam-dabam cikin makon, kuma a yanzu haka sansanin na hannun mayakan da ke kiran kansu ‘yan “burged na 7,” da ke da mazauni a Tarhouna ne.

To amma Ahmed Maitiq, Mataimakin Shugaban Gwamnatin Hadin Kan Kasa Ta Libiya, ya ce an tura wasu burged-burged masu goyon bayan gwamnatin hadin kan kasar, su sake kwato sansanin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG