A Najeriya Mata Fiye Da Dubu 40 Suke Mutuwa A Lokacin Haifuwa Ko Wace Shekara

Ma'ikatan ungozoma da ake karancinsu a Najeriya.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya tace fiyeda mata dubu arba'in ne suke mutuwa ko wace shekara a Najeriya lokacin haifuwa.
Kwarraru da masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya sun gabatar da kasidu a wani taron wayar da kan juna domin tunawa da zagayowar ranar ungozoma ta duniya.

Shekaru ashirin da biyu da suka wuce na Majalisar dinkin Duniya ta kebe wannan rana 6 ga watan Mayu na kowace shekara domin kara jawo hankali kan aikin ungozomomi a fadin duniya, da nufin karfafa masu gwiwa saboda a cimma muradun karni na 4 da na 5 kafin shekara 2015.

To wani irin kalubale ne unguzomi a Najeriya ke fuskanta? Kuma ta wace hanya za'a magance su?

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoto kan aikin Ungozoma