Accessibility links

Taluaci Yana Daga Cikin Dalilan Tashe Tashen Hankula A Najeriya-Ka'oje

  • Aliyu Imam

Wani sashen Baga da aka kona sakamakon rikici da ya barke a yankin a baya bayan nan.

Tsohon ministan harkokin wasanni Bala Bawa Ka'oje, wanda kuma shine ma'ajin jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya yace kwararru suna danganta tashe tashen hankula dake aukuwa a najeriya kan talauci.

Ma'ajin jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya kuma tsohon ministan harkokin wasanni na Najeriya Alhaji Bala Bawa Ka'oje, yace akwai dalilai masu yawa da suke janyo yawan tashe tashen hankula a Najeriya.

Tsohon ministan wanda ya furta haka a hira da aka yi da shi lokacinda ya ziyarci sashen Hausa na Muriyar Amurka ranar litinin na makon nan, duk da haka yace gwamnati tana daukan matakai na kwarai wajen magance wasu daga cikin korafe korafen mutane cewa shugaban kasa ya fi maida hankali kan yankin da ya fito.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG