Mata Sun Fara Kasuwar Baje Koli a Nijer

NIGER: Matan kasar

An bude wata kasuwar baje koli a Jamhuriyar Nijer, inda matan kasar suke bayyana basirarsu ta kere kere ga mahalarta da sauran duniya baki daya, a bbabban birnin kasar Niamey.

Mata masu kere kere kayayyakin gargajiya sune galibin wadanda suka baje kolinsu a wannan kasuwar ta SAFEM a takaice, wanda aka shirya a karo na goma da zummar bunkasa sana’o’in matan kasar.

Gwamnatin kasar da ta kirkiro wannan kasuwar baje kolin tace wannan kasuwar zata karfafa mu’amala da huldar kasuwanci tsakanin matan kasar Nijer da takwarorinsu na sauran kasashen Afrika.

Wannan kasuwar baje kolin na bana ya tattaro mata mahalarta daga kasashe dake makwabtaka da jamhuriyar Nijer. Mata da dama daga sassan kasar da ma na kasashen ketare sun baje kayayyakin kere kere da na fasaha kana suka yabawa gwamnatin Nijer da irin gudnmuwa da take yiwa kasuwancin mata.

Your browser doesn’t support HTML5

NIGER ARTS EXHIBITION