Matakin Kona Na'urorin Hakar Ma’adinai Na Haifar Da Rikici Tsakanin Wasu Fararen Hula Da Sojoji A Ghana

HAKAR MA'ADINAI

Matakin kona manyan na'urorin hakar ma’adinai a kasar Ghana da sojoji su ka dauka na janyo cece kuce tsakanin wasu al’umma inda wasu ke ganin hakan na haifarda tsami tsakanin fararen hula da dakarun soja a kasar.

Mallam Musannan na ganin kamata ya yi gwamnati ta ringa anfani da na’urorin muddan an kama gurin kwashe rairayi a cikin magudanan ruwa maimakon a kona su. Wannan ra'ayi na al’umman na zuwa ne biyo bayan taho mu gama tsakanin sojoji da wasu matasa a j ahar Ashanti a daidai lokacinnda sojojin suka kona na'urorin hakar ma’adinai har gobarar ta fadada zuwa wani gida har gidan ya kone kurmus.

Yayin jawabinsa da muryar Amurka, Mallam Irbad Ibrahim mai sharhi kan harkar tsaro ya ce kamata ya yi sojojin su sauya matakin tunkurar masu hakar ma’adinai ta barauniyar hanya tunda matakin kona na'urorin tono din ya ci tura.

HAKAR MA'ADINAI

Mallam Yahya daya daga cikin masu hakar ma’adinai da manyan na'urorin tono ya roki gomnati da ta sauya matakin saboda su na zuba zunzurutun kudade ne domin sayo na'urar hakar ma’adinai din.

Sai dai kuwa shugaban sojojin a yankin jihohin arewa Gabriel Aphor yace matakin da suka dauka na kona na'urorin shi ne mafita kuma ba kasafai su ke kona na'ura ba sai sun tabbatar da cewa na'urar ana aiki da ita ta haramtaciyar hanya.

Shi kuwa Alhaji Musah Shekayi daya daga cikin jami’an sadarwa na jam’iyyan NPP mai mulki a Ghana, cewa ya yi tuni gomnati ta dakatarda kona naurar.

Hakar ma’adinai ta barauniyar hanya na daga cikin abubuwan da ke gurbata ruwan sha da kasa tare da yanayin sararin samaniya a kasar Ghana a bin da gwamnati ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin da ta ke yi na shawo kan wannan matsala.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Matakin Kona Naurorin Hakar Ma’adinai Na Haifarda Tsami Tsakanin Wasu Fararen Hula Da Dakarun Soja A Ghana