Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CONGO: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wasu ‘Yan China 5 Ma'aikatan Hakar Ma'adinai


Yan bindiga

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in dan sanda tare da yin garkuwa da wasu ‘yan kasar China biyar da ke aiki a wata mahakar zinari a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango jiya Lahadi, kamar yadda majiyoyin soji suka bayyana.

Kakakin rundunar sojojin yankin Manjo Dieudonne Kasereka ya bayyana cewa, da misalin karfe biyu na safe, wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka kai wa sansanin 'yan China din hari a kauyen Mukera da ke yankin Fizi na lardin Kivu ta Kudu.

“Mutum 14 ne maharan suka tafi da su, biyar daga ciki, an kai su zuwa wani wuri da ba a san inda suke ba,” in ji shi, ya kara da cewa sauran taran kuma an kwashe su kuma suna cikin koshin lafiya.

Kanal David Epanga, shugaban rundunar soji a Fizi, ya ce dan sanda daya ya rasa ransa a harin.

Ma'aikatan 'yan kasar China biyar da aka sace, ma'aikatan wani kamfani ne da ke aikin hakar gwal a yankin na tsawon watanni hudu zuwa biyar, in ji shugaban kungiyoyin fararen hulan Fizi, Lusambya Wanumbe.

A cikin watan Agusta, hukumomin Kivu ta Kudu sun dakatar da ayyukan kamfanonin da ke samun kudi daga China, bayan da mazauna yankin suka zarge su da hako zinari ba tare da izini ba da kuma lalata muhalli.

Dubi ra’ayoyi

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG