Matan Arewacin Najeriya Suna Baya ta Fuskar Ilimi- Yelwa Goje

Wadansu yammata a makaranta.

Hajiya Yelwa Danjuma Goje ta bayyana takaicin koma bayan ilimi arewacin Najeriya musamman tsakanin ‘ya’ya mata.

Uwargidan tsohon gwamman jihar Gombe Hajiya Yelwa Danjuma Goje ta bayyana takaicin koma bayan ilimi arewacin Najeriya musamman tsakanin ‘ya’ya mata.

A cikin hirarta ta Grace Alheri Abdu yayin ziyarar da ka kawo Sashen Hausa na Muryar Amurka, Hajiya Yelwa tace kowa ya sani Arewacin Nigeria, mata na baya, duk da yake an sami ci gaba fiye da yadda lamarin yake a da. Sai dai tace idan aka kwatanta da kudancin Nigeria za a ga cewar matan Kudancin kasar sun fi na arewa cigaba.

Hajiya Yelwa tace abinda yake kawo cikas da ya zame kadangaren bakin tulu a ilimin mata sun hada da addini, da al’adu da ma talaucii sai dai tace duk da haka yanzu idan aka shiga yankunan karkara sai a tarar ana kokari kauyuka ana dan kokari amma ba kamar da ba.

Takara da cewar matan arewa da sauran rana akaba, ta kuma ce yanzu ana kan wayar da kan iyaye sun domin kara bada goyon baya hadin kai.

Ga cikakkiyar Hirar

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Hajiya Yelwa Danjuma Goje