Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Su Na Gwabzawa Da 'Yan Boko Haram A Gamboru-Ngala


Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa ana gwabza fada a garin Gamboru-Ngala, dake dab da bakin iyaka da kasar Kamaru a Jihar Borno.

Shaidu sun ce ‘yan Boko Haram sun kai farmaki a kan garin a yau litinin da safe, inda suka dirkaki caji ofis na ‘yan sanda da kuma sansanin sojan dake garin.

Suka ce wasu daga cikin sojojin Najeriya sun tsallaka cikin Kamaru a bayan da harsasansu suka kare, inda sojojin Kamaru suka ba su mafaka. Akwai rahotannin dake cewa sojojin na Kamaru su na dafawa sojojin Najeriya wajen yakar ‘yan ta’addar na Boko Haram.

A halin da ake ciki, kungiyar Boko Haram ta ce ta kame wani gari a arewa maso gabashin Najeriya kuma ta hada shi da abinda ta kira Daularta ta Islama.

Sanarwar tana kunshe cikin wani sabon bidiyon da aka fitar jiya lahadi, inda aka nuna mutumin da ake ikirarin cewa shine shugaban Boko haram, Abubakar Shekau, yana cewa sun kama garin Gwoza na jihar Borno kuma ya zamo bangaren daularsu.

A cikin wata hirar da yayi da VOA, kakakin rundunar sojojin, manjo Janar Chris Olukolade ya karyata ikirarin kungiyar yana mai cewa babu abinda ya taba diyauci ko kuma wani yanki n kasa na najeriya.

Yace sojoji su na ci gaba da damarar kwato garin na Gwoza.

Boko Haram ta kashe dubban mutane tun daga 2009, a bisa ikirarin cewa wai tana so en ta kafa daular Islama a arewacin najeriya.

Duk da dokar ta bacin da aka kafa a Borno da wasu jihohi biyu makwabta, hukumomin najeriya sun kasa tabuka wani abu wajen murkushe kungiyar wadda masu fashin baki suka ce tana da makamai fiye ma da sojojin gwamnati.

A makon jiya wasu sojojin Najeriya sun ce wata bataliyar da aka tura Gwoza da Dalwa ta ki tafiya can a saboda sojojin sun ce ba su da makaman da suka kamata.

XS
SM
MD
LG