Matasa da Suka Samu Horaswar YALI a Amurka na Rawar Gani a Najeriya

Masu halartar taron YALI shekarar 2014

Bisa ga yunkuri na shugaban kasar Amurka Barak Obama, na ganin gwamnatin Amurika karkashin jagorancin shi, ta taima kama kasashen Afrika, a shekarar da ta gabata ya kaddamar da wata gidauniya me suna (Mandela Washington Fellowship) a turance, wada aka kawo matasa maza da mata, da ga kasashen Afrika a kowane irin fanni rayuwa ta yau da kullun, wanda aka koyar da su na wasu tsawon satutuka gomasha hudu (14). A ilahirin jami’o’in kasar Amurika.

Awannan karon wadannan matasan an koyar da su a fannonin sanin makar shugabanci, kasuwanci, da tattalin arzikin kasa. A wata tattaunawa da mukayi da daya daga cikin waddanda suka samu halartar wannan kwas in a shekarar 2014 da ta gabata, yayi muna Karin haske dangane da wannan horaswar.

Yace sun samu halartar wannan horaswar kuma an koyar da su a kan makamar shugabanci na gari mai adalci, da kuma hanyoyin da zasu iya dogaro da kai, kana da hanyar da zasu bi su zamo ‘yan kasa nagari, wannan dai yasa sun ziyarci ma’aikatan gwamnatin Amurika inda suka ga yadda ake gudanar da aiki da kuma yada ake mu’amala da jama’a ta hanyar gogewa da mutunta juna. Cikin bayaninsa yayi nuni da cewar bayan komawarsu kasashen su musamman ma Najeriya sunyi kokarin hada kawunansu don aiwatar da abun da suka koyo a Amurika, sai da wani tsaiko da suke samu kasancewar mafi akasarinsu suna aiyukansu a wurare da-ban-da-ban, wannan yasa basu samu damar gabatar da wani aiki kai tsaye ba.

Amma duk da haka a matsayinsa na Likita sun hada wata kungiya da shi da wata abokiyar da sukasamu horaswa daya a Amurika me suna Maryam Muhammad, wada take da wata kungiya me zamankanta, wadda suke taimakama mutane masu karamin karfi, don taimakon wannan al'umar tasu, bisa wannan hadin kan sun samar da makudan kudi da har akasamu damar akayima kimanin mutane ashirin (20) aikin ido masu karamin karfi a nan jihar Kano.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan da suka samu horaswar YALI a Amurka na rawar gani a Najeriya- 1'46"