Matasa Sun Kona Gidan Shugaban ANPP A Maiduguri

Wasu matasa 'yan banga suka tsaya don a dauki hotonsu a Maiduguri, 11 Yuni, 2013.

Haka kuma wadannan matasa 'yan banga masu farautar 'yan Boko Haram, wadanda ake kira "Civilian JTF" sun kai farmaki kan gidan tsohon gwamna Ali Modu Sherrif
A Maiduguri, hedkwatar Jihar Borno, matasa dauke da adduna da sanduna sun kai farmaki a kan gidan shugaban jam'iyyar ANPP na jihar, Alhaji Mala Othman, suka cinna wuta suka kona.

Wadannan matasa 'yan banga, wadanda suka kunno kai cikin 'yan kwanakin nan da sunan farautar 'ya'yan kungiyar Boko Haram a garin, sun abka gidan shugaban jam'iyyar tunda hantsin jiya litinin, inda suka farfasa kafin su cinna masa wuta.

An ga 'yan sanda sun fita da wasu mutane cikin mota daga wannan wuri, kuma ana kyautata zaton cewa Alhaji Mala Othman ne da iyalansa.

Daga nan, wadannan matasa, wadanda yawansu ya kai kimanin dari biyu, sun zarce zuwa gidan tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sherrif, inda suka yi fashe-fashe. Wakilin Sashen Hausa, Haruna Dauda, ya dauki muryar wasu daga cikin matasan su na kira ga jama'a da su bunka ma gidan wuta.

Jami'an tsaro sun bayyana, inda suka fara yin harbi a sama domin tarwatsa gungun matasan.

Tun lokacin da wadannan matasa da ake kira "Rundunar JTF ta Farar Hula" suka kunno kai, jama'a sun yi kashedin cewa su na iya zamowa wata sabuwar matsalar a wannan gari da ya kasa jin sakat.

Wakilin sashen Hausa, Haruna Dauda, ya bi wadannan matasa yana daukar abubuwan da suke faruwa har zuwa lokacin da jami'an tsaro suka fara harbi domin tarwatsa su a garin na Maiduguri, ga kuma yadda abubuwan suka kaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa Sun Kai Farmaki Gidan Modu Sherrif, Sun Kona Gidan Shugaban ANPP Na Jihar Borno - 2:38