Matasa Sun Yi Taron Koli a Taraba

Matasa suna kona tayoyi a zanga zangar kin jinin janye rangwamin man fetir.

Majalisar Matasa a Najeriya da gwamnatin Jihar taraba suka shirya wannan taron don fadakar da matasa kan yadda zasu kaucewa fadawa tarkon ayyukan banza
Matasa a Jihar Taraba sun gudanar da taron koli kan yadda za a iya tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a tsakaninsu, da kaucewa fadawa tarkon baragurbin 'yan siyasa dake amfani da su domin tayar da fitina.

Majalisar Matasa a Najeriya da kuma gwamnatin Jihar Taraba suka shirya wannan taron domin a samu hanyoyin samarwa da matasa sana'o'in da zasu kawar da hankulansu daga shiga ayyukan rashin da'a da koyan zaman tare da juna cikin lumana.

A wajen wannan taron, kwararru da shugabanni da sauran jama'a duk sun yi jawabai kan muhimmancin zaman tare. Shugabannin matasa a Taraba sun ce zasu yi kokarin tabbatar da cewa 'yan'uwansu matasa ba su zamo karnukan farautar 'yan siyasar dake neman cimma gurinsu ta hanyar amfani da matasan domin aikata laifi ba.

Suka ce muhimmin abu shi ne tabbatar da cewa matasa sun yi zaman tare da junansu ba tare da bambancin addini ko kabila ko bangare ba.

Shugabanni a jihar, cikinsu har da mukaddashin gwamna Garba Umar, yace sun debi matasa masu yawan gaske domin samar musu da ayyukan yi da nufin kaucewa yiwuwar fadawarsu cikin ayyukan bangar siyasa.

Ibrahim Abdulaziz ya aiko da cikakken bayani kan wannan taron.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa Sun Yi Taron Koli A Taraba - Rahoton Ibrahim Abdul'aziz - 3:34