Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Cikin Kayan Soja Sun Kashe Mutane 19


Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, zaune a tsakiya, tare da 'yan bindigar kungiyar.
Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, zaune a tsakiya, tare da 'yan bindigar kungiyar.

Shaidu sun ce 'yan bindigar da suka yi shigar sojoji sun kafa shingen bincike a kan hanya yau lahadi kusa da bakin iyaka da Kamaru suka rika yanka mutane

Shaidu sun ce wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne, sun kashe mutane 19 yau lahadi a wani wurin binciken karya irin wanda sojoji ke kafawa kan hanya a kusa da bakin iyaka da Kamaru.

Wasu mutanen da suka kubuta da rayukansu tare da shaidu a kusa da wurin sun ce an tsinci gawarwakin mutane 19, cikinsu har da wasu direbobin manyan motoci biyu, a wurin da 'yan bindigar suka yi kwanton-bauna a kusa da garin Logumani, kimanin kilomita 30 daga bakin iyaka da Kamaru.

Shugaban wata kungiyar banga fararen hula mai tallafawa gwamnati a yaki da 'yan Boko Haram, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa biyar daga cikin mutanen an harbe su ne da bindiga, sauran 14 kuma yanka su aka yi.

Wasu rahotannin sun ambaci shaidu da wadanda suka kubuta da rayukansu su na fadin cewa 'yan bindigar sun daina kashe mutane ne kawai suka gudu a kan babura abayan da daya daga cikinsu ya samu kira a waya, watakila ko an fada musu cewar ga jami'an tsaro tafe ne.

Wani mutum guda ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa har an fito da shi daga cikin mota za a kashe shi, sai wayar dan bindigar ta buga, kuma da ya amsa sai suka hau babura shi da sauran 'yan bindigar suka gudu.

Yace sun cinna wuta ma motoci guda biyar a wurin kafin su gudu.
XS
SM
MD
LG