MAWAKAN SLAM SUN GARGADI MATASA A KAN MUHIMMANCIN NEMAN ILIMI

MAWAKA

An gargadi matasa a kasashen Afirka ta yamma cewa su dukufa wajen neman ilimi, maimakon jefa rayukan su cikin hadari ta neman zuwa turai ala tilas.

Wannan gargadi yana daga baitocin wakoki da mawaka daga wasu kasashen Afrika ta Yamma masu amfani da truancin Faransa suka rera a wani taron buki a dandalin raya al’adu da nishadi na jami’ar Abdul Mumin ta Niamey a Jamhuriyar Nijer.

Mawakan masu rera wakokin gargadi da suke amfani da salon kahiya sun fadakar da matasa a kan muhimmancin neman ilimi a maimakon jefa rayuwarsu cikin hadari suna ketarawa zuwa kasashen waje ta barauniyar hanya.

Mahalarta bukin wakokin fadakarwar da da ake kira SLAM a takaice sun shirya baitocin wakoki da kalamai masu ratsa jiki suka jan hankalin matasa da suka zo kallo wadanda galibinsu dalibai ne a kan illolin amfani da barauniyar hanya zuwa ci rani.

Hukumar karfafa zaman lafiya ta kasa da hadin gwiwan Kungiyar Tarayyar Turai ne suka dauki dawainiyar shirya wannan taron bukin.

Your browser doesn’t support HTML5

NIGER MUSICAL FESTIVAL