MDD Ta Kakabawa Mutanen Libya 6 Takunkumi Bisa Laifin Safarar Mutane

Safarar mutane ta tekun Meditarranean

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, MDD ya kakabawa wasu mutane shida dake Libya akan safarar mutanen dake kokarin zuwa Turai suna ketarawa dasu cikin tekun Mediterranean

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya MDD, ya ayyana mutane 6 wadanda suke safarar mutane domin a aza musu takunkumin kasa da kasa saboda amfani da dubban 'yan ci rani da suke bi ta gabar ruwan Libya.

Mutanen shida,4 'yan kasar Libyan ne, biyu kuma 'yan kasar Eritrea ne wadanda suke shugabantar kungiyoyin batagari da 'yan banga, suna cin karfin 'yan ci rani daga kasashen Afirka dake kokarin ketara tekun Mediterranean zuwa Turai. Takunkumin ya fara aiki daga jiya Alhamis. Matakin zai hana su amfani da ajiyar su a bankuna, da kuma hana su yin balaguro zuwa kasashen ketare.

Wannan shine karon farko da kwamitin sulhu zai aza takunkumi kan shugabannin kungiyoyi 'yan banga masu aikata laifi ciki harda safarar mutane.