Najeriya: An Dauki Matakin Kawo Karshen Rikicin Kabilanci Da Addinin

Wani jami'in tsaron farin kaya na SSS a Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tura wani sashe na kwararrun ‘yan sanda a bangaren kwantar da tarzoma da yaki da ta’addanci zuwa Zaki Biam, a jihar Benue, don magance fitinar da ta auku kwanannan inda wasu su ka farwa jama’a da hakan ya kai ga asarar rayukan da dukiyoyi.

Yunkurin aikin dawo da zaman lafiya a yankin na tsakiyar arewacin Najeriya ya hada har da kwararrun karnuka da aka horar da su da kuma jirage masu saukar ungulu domin ganin dukkan shiyyar daga sama.

Hakan na zuwa a daidai lokacin da ma’aikatar harkokin cikin gida karkashin Janar Abdulrahman Dambazau, mai ritaya ta dawo da bincikien asalin baki a kowane yankin, ta hanyar amfani da jami’an shigi da fice da masu sarautar gargajiya.

Rundunar ‘yan sandan ta yi amfani da jami’anta na musamman zuwa yankin Kaduna ta kudu dan hana fitinar kabilanci da banbancin addini dake haifar da asarar rayuka da dukiyoyi da dama.

Daga Abuja, ga cikakken rahoton da Medina Dauda ta aiko mana.

Your browser doesn’t support HTML5

'Najeriya: An Dauki Matakin Kawo Karshen Rikicin Kabilanci Da Addinin