Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hare-Haren Kunar-Bakin-Wake A Kusa Da Tashar Muna


Harin Kunar Bakin Wake Kusa da Garejin Muna a Maiduguri

Wadannan hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 tare da 'yan kunar bakin waken a wani sansanin 'yan gudun hijira da suka fito daga Gulumba a kusa da tashar motar Muna.

'Yan kunar-bakin-waken da ake kyautata zaton cewa 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kan wasu sansanonin 'yan gudun hijira dake kusa da tashar motar Muna a Maiduguri, cikin daren da ya shige.

Wannan hari na baya bayan nan yayi sanadiyyar mutuwar maharan da kuma wasu mutane hudu, wadanda suka hada da wata mace da dan karamin yaro.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta Jihar Borno, yace maharan sun tayar da bama bamai a wurare dabam-dabam, inda a kowane wuri suka kashe mutum guda daya, yayin da a na ukun suka kashe wannan mata da yaro.

An sha kai hare-haren ta'addanci na kunar bakin wake a kusa da wannan tashar mota ta Muna, wadda take bayangari a Maiduguri idan mutum ya fito daga garuruwa kamar Mafa, Dikwa ko gamboru-Ngala, kuma a inda ake shiga motar zuwa wadannan garuruwan.

Ga rahoton da Hussaina Mohammed ta aiko mana daga Maiduguri

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG