Najeriya: Kama Karya Wayen Tsayar Da ‘Yan Takara Na Mayar Da Hannun Agogo Baya

hotunan yan siyasa

Jam’iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da gudanar da zabukan cikin gida domin fitar da ‘yan takarar mukamai daban-daban a babban zaben kasar da aka shirya gudanarwa cikin watan Fabarairun badi.

Sai dai masana kimiyyar siyasa da kwararru game da lamuran shari’a da dokokin ‘kasa na cewa, yanayin karfa-karfa da kama karya wajen tsayar da ‘yan takara na mayar da hannun agogo baya ga ci gaban dimokaradiyyar Najeriya.

A lahadin nan ce jam’iyyun PDP da APC sukayi zaben cikin gida domin fitar da ‘yan takarar kujerar gwamna a galibin jihohin kasar, bayan da APC tayi zaben fitar da dantakarar shugaban ‘kasa ta hanyar zaben kai tsaye.

Tuni dai sakamakon zaben ya fara bayyana awasu jihohi, ya yin da takaddamar zafin bukata da zargin dauki dora ta sanya jam’iyyun suka dage zaben a wasu jihohin.

Ko a jiya Litinin sai da tsagin Kwankwasiyya na jam’iyyar PDP yayi yunkurin gudanar da zaben fitar dantakarar gwamnan Kano, amma ‘yan sanda suka hana bisa dalilin cewa, uwar jam’iyyar ta ‘kasa ta dage zaben a Kano da Lagos da kuma Imo, bugu da kari dama akwai odar kotu kan takaddamar shugabanci.

A jam’iyyar APC ma zabe ya gagara domin fitar da ‘yan takarar gwamna a wasu jihohin wadanda suka hada da Zamfara da Lagos

Masu kula da lamura dai na ganin sarkakiyar dake tattare da tabbatar da magudin zabe a gaban kotu, na sanya ‘yan siyasar Najeriya su zabi a kai su kara maimakon su kai.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Kama Karya Wayen Tsayar Da ‘Yan Takara Na Mayar Da Hannun Agogo Baya - 3'47"