Najeriya: Shin Cigaba Aka Samu Ko Akasinsa a Shekara 5 Na Mulkin APC?

A yayin da gwamnatin jam’iyyar APC a Najeriya ke cika Shekara biyar da kama ragamar mulkin kasar, 'yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu a kan cigaba ko akasin hakan da aka samu a tsawon wadannan shekaru.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi ikirarin samun nasara a yaki da cin hanci da kuma karya lagon ‘yan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Sai dai a gefe guda akwai matsalar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da ke ci gaba da yi wa jama’a kisan gilla a yankin jihohin arewa maso yammacin kasar da kuma wasu jihohin arewa maso tsakiyar Najeriya.

Jihar Neja, da ke arewa ta tsakiyar Najeriya na daya daga cikin jihohin da ke fama da irin wannan matsala.

Alhaji Murtala Maigyada, shugaban kungiyar Muryar Talaka a jihar kuma mai fafutukar kare hakkin talaka, ya ce ko da ya ke a baya an samu nasara a yaki da ‘yan kungiyar ta Boko Haram, har yanzu akwai babbar matsala ta ‘yan bidiga.

Hukumomi dai a matakai daban daban sun ce suna kokarin kawar da 'yan bindigar, kamar yadda kwamishinan yada labaran jihar Neja Alhaji Muhammadu Sani Idris ya bayyana a wani taron manema labarai da aka yi game da ranar Demokradiyya.

Bayan matsalar ‘yan ta’adda, matsalar annobar cutar coronavirus da ta fado kwatsam ta yi matukar dagula al’amurra ga mahukuntan Najeriya, inji gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Shin Ci Gaba Aka Samu Ko Akasinsa a Shekaru 5 Na Mulkin APC?