Najeriya ta dauki matakin tsaftace labaran da kafofin sadarwan zamani ke yadawa-IBB

Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB

A wata firar da tsohon shugaban Najeriya ya yi da Muryar Amurka Janar Ibrahim Badamasi Babangida ko IBB yace ya zama tilas gwamnatin Najeriya ta dauki matakin tsaftace labaran da kafofin sadarwan zamani ke yadawa wannan ko ya biyo bayan labarin da suka buga makon jiya cewa shugaban ya rasu

Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ko IBB a takaice, yace ya zama tilas gwamnatin Najeriya ta mataki akan kafofin sadarwa na zamani domin tsaftace irin labaran da suke bugawa.

A firar da ya yi da Muryar Amurka tsohon shugaban yace dokar nan da majalisar dattawan kasar ta so kafawa kwanakin baya da zummar takaita kafofin sadarwa na zamani zata taimakawa kasar wajen tsaftace labarun da suke fitarwa.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi karin haske akan bada labarin mutuwarsa alhali kuwa yana raye. Yace shi musulmi ne kuma ya yi imani da abun da Allah ya fada cewa duk wani mai rai zai mutu. Saboda haka ba wani abun mamaki ba ne.

Tsohon shugaban da ya kwashe shekaru takwas yana mulkin Najeriya yace yana alfahari da tada hedkwartar mulkin Najeriya daga Legas zuwa Abuja a lokacin mulkinsa. Ya godewa Allah da kuma mutanen Najeriya da suka bashi goyon baya. Yace akwai mutane da yawa da basu yi tsammanin Abuja zata yiwu ba.

Daga karshe ya yiwa mutanen Najeriya fatan alheri yana cewa duk halin da suke ciki yanzu Ubangiji Allah zai kawo saukinsa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya ta dauki matakin tsaftace labaran da kafofin sadarwan zamani ke yadawa-IBB - 3' 29"