Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, ya karyata labarin mutuwarsa


Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB.

Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ko IBB ya karyata labarin da ake bazawa ta kafofin sadarwa na zamani tun ranar Asabar cewa ya mutu

Labarin da aka dinga bazawa ta kafofin zamani tun ranar Asabar da ta gabata ya jefa 'yanuwa da masu kaunar shugaban da abokan arziki cikin rudani.

Jiya Lahadi tsohon shugaban ya kira taron manema labarai inda ya bayyanawa kowa cewa yana nan raye bai mutu ba. Yace a matsayinsa na musulmi ya san cewa kowanene mutum sai ya mutu. Saboda haka duk wanda yake da rai yana jiran mutuwa ne. Mutuwa zata zo idan lokacinta ya yi. Yace ba'a yiwa mutum gorin mutuwa ko kaddara.

Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya yiwa wadanda suka dinga kira suna tambaya godiya saboda kaunar da suka nuna masa da iyalansa.

Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun labarin karya a kafofin sadarwa na zamani al'amarin dake jefa dimbin jama'a cikin halin rudani.

Masana harkokin sadarwa na ganin yakamata hukumomi su yi masu iyaka.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG