Najeriya Ta Yi Rawar Gani a Afirka cikin Shekaru 55 da Ta Samu 'Yanci - Dattawan Arewa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Yayinda Najeriya ke bikin cika shekaru 55 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya wasu dattawan arewa sun yaba da rawar da ta taka musamman a nahiyar Afirka

Kasar ta taka rawar gani a yakin neman cin gashin kai da wasu kasashen Afirka suka yi. Najeriya ta taimaka masu har suka cimma nasara.

Ta kuma yi abun a zo a gani wurin shiga tsakanin kasashe dake fama da rikicin cikin gida a nahiyar Afirka.

Yin la'akari da hobasan da Najeriya ta yi a Afirka ya sa dattawan suka baiwa Najeriya matsayin jagora a fannin diflomasiya.

Ambassador Wilberforce Juta tsohon gwamnan jihar Gongola a jamhuriya ta biyu wadda yanzu ta zama jihohin Adamawa da Taraba yace nasarorin kasar da ta cimma cikin shekaru 55 sun baiwa sauran kasashe mamaki na cigaba da kasancewa dunkulalliyar kasa bayan yakin basasa.

Yace bayan yakin basasa a karkashin shugabancin Janar Yakubu Gowon kasar ta farfado kuma tattalin arzikinta ya bunksa. Wasu da suka yi tsammanin kasar zata wargaje sun sha mamaki.

Shi ma da yake furuci kan kiman Najeriya a idanun duniya tsohon ministan ilimi a karkashin shugaba Sani Abacha Alhaji Dauda Birma yace canjin mulkin da aka samu a zaben da ya gabata ya farfado da martaba da kuma mutuncin Najeriya a matsayin jagora ta fuskar diflomasiya.

A fannin da ya shafi tattalin arzikin kasa da kasa Najeriya ta taka rawar a zo a gani wajen kafa kungiyar tattalin arziki na kasashen Afirka ta yamma inji shugaban kungiyar 'yan kasuwan nahiyar Afirka Alhaji Bamanga Tukur.

Masani kan harkokin diflomasiya Abdulhamid Song yace nasarorin da kasar ta samu cikin shekaru 55 da ta samu 'yancin kai sun ta'allaka ne akan hadin kai da zaman kasar tsintsinya madaurinki daya.

Ga rahoton Sanusi Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ta Yi Rawar Gani a Afirka cikin Shekaru 55 da Ta Samu 'Yanci - Dattawan Arewa - 3' 16"