Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya ce Gwamnati ta Kudiri Aniyar Yin Abubuwan a Tsanake Bisa Tsari


Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a ECOWAS, 23 Satumba, 2015.

Manjo Ibrahim Abdullahi Yusuf, na runduna ta 177, dake tsaron fadar shugaban Najeriya, wato “Guard Brigade” ne ya jagoranci faretin bikin ranar samun ‘yancin kai a fadar shugaban Najeriya, ta ASo Rock, dake Abuja.

Kwamnadan dakarun da aka canza da wanda ke karbar aiki a fadar sun yi fareti tare da askarawan nasu, faretin da ya hankalin shugaba Buhari, da har saida ya tafa masu.

Sojojin sun yi fareti iri daban daban amma bisan ga dukkan alamu faretin bebaye da ba’a Magana a cikinsa mai suna “silent drill”shi yafi jan hankalin manyan baki masaamman tsohon shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon, a lokacin ake gani kamar zakamisa na gidan Soja ya motsa.

Tun da farko sai da shugaba Buhari, ya yiwa ‘yan Najeriya,jawabi da sanyin safiyar yau inda ya tabo batutuwa da dama inda ya magantu bisa nadin Ministoci.

Ya ce ya ‘yan uwa ‘yan Najeriya, an yi ta zumudi da jiran bayyana Ministici, ba wani hujjar yin zumudin Gwamnati ta kudiri aniyar yin abubuwan a tsanake bisa tsari sai zama riga Malam Masallaci mu bayyana sunayen ministoci ba’a kamala tantance ma’aikatun da za’a bari ba.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00

XS
SM
MD
LG