Nigeria da Kamfanin Man Shell

  • Aliyu Mustapha
Katafaren kamfanin man Royal Dutch Shell ya ce ba zai iya sayarwa kasashen waje wani nau’in danyen mai, mai matukar inganci daga Najeriya ba.

Katafaren kamfanin man Royal Dutch Shell ya ce ba zai iya sayarwa kasashen waje wani nau’in danyen mai, mai matukar inganci daga Najeriya ba kamar yadda ya yi alkawari saboda yawan hare-haren da ke lalata mi shi bututun mai. Wani kakakin kamfanin ya fada a yau laraba cewa kamfanin ya ayyana kasa cika alkawari saboda abun da ya fi karfin shi. Hakar nau’in man da ake kira, Bonny Light, wanda wannan al’amari ya shafa, shi ne babban aikin Shell a Najeriya.

A ranar Lahadin da ta gabata, kamfanin Shell ya bada labarin cewa a cikin watan nan na Agusta kadai, sau ukku ana kai hari kan wani bututun shi da ke Bonny, kuma ya ce irin wadannan hare-hare sai karuwa su ke yi. Kamfanin ya ce a cikin duka hare-haren ukku da aka kai, barayi sun huhhuda bututun ko kuma sun yanke shi da zarto don a janye man da ke bi ta bututun.