Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Man Shell Yace Ana Kara Kai Hare-Hare Kan Bututunsa


Taswirar yankin Niger-Delta a kudancin Najeriya

Kamfanin man na Shell ya ce sau uku ke nan a cikin wannan wata na Augusta ana kai hari a kan bututunsa da ya taso daga Cawthorne Channel zuwa Bonny.

Kamfanin mai na Shell yace ‘yan fasa-kwabrin mai ne suka haddasa kwararar man da aka samu cikin wannan makon a yankin Niger Delta na kudancin Najeriya, kuma irin wadannan hare-hare su na karuwa.

A cikin wata sanarwar da ya bayar jiya lahadi, kamfanin na Shell ya ce sau uku ke nan a cikin wannan wata na Augusta ana kai hari a kan bututunsa da ya taso daga Cawthorne Channel zuwa Bonny. Kamfanin na Shell yace a wadannan hare-hare uku, barayin mai su na huda bututun, ko kuma su na amfani da zarto wajen yanka shi domin su saci mai.

Kamfanin Man Shell Yace Ana Kara Kai Hare-Hare Kan Bututunsa
Kamfanin Man Shell Yace Ana Kara Kai Hare-Hare Kan Bututunsa

Kamfanin yace a bayan hari na baya-bayan nan, ya dakatar da tura mai ta wannan bututun domin hana shi yoyo, yana kuma aikin gyara wannan bututu tare da kwashe man da ya zuba. Kamfanin bai bayyana yawan man da ya zube ba, haka kuma bai bayyana irin illar da wadannan ayyuka na zagon-kasa suka yi ga yawan man da Shell ke samarwa daga Najeriya ba.

A cikin sanarwar ta jiya lahadi, kamfanin Shell yayi ikirarin cewa kashi 98 cikin 100 na dukkan man da ya tsiyaye a 2009, barayin mai ne suka haddasa shi, amma yace ya kwashe dukkan man ba tare da la’akari da abinda ya haddasa shi ba.

XS
SM
MD
LG