Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Goodluck Jonathan ya Sanya Hannu kan Dokar Zabe.


Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan, ya rattaba hannu kan daftarin sabuwar dokar zaben da za’a gudanar shekara maizuwa a Nigeria.

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria a jawabinsa na kafinsanya hannu kan daftarin dokar zaben ran Juma’a yace sanya hannu kan daftarindokar zaben hakan ya baiwa hukumar zaben Nigeria (INEC) damar shiryawa da fidda tsarin yadda za’a sabunta rajistar masu kada kuri’a da yadda jam’iyyun siyasa zasu bada sunayen ‘yan takara da fara gangamin zabe.Shugaba Goodluck Jonathan yace sabuwar dokar zaben na kunshe da sauye-sauyen da zasu taimaka wajen inganta tsarin zabe a Nigeria, don haka yayi kira ga ga ‘yan Nigeria das u bada cikakken hadin kansu domin samun nasarar gudanar da zaben cikin ‘yanci da walwala.

XS
SM
MD
LG