Nijar: An Fara Taron Nazarin Gudunmawar 'Yan Jarida Don Cimma Kudurori

Nijar: Taron Kungiyar SIMED A Birnin Yamai

A jamhuriyar Nijar ‘yan jarida daga kasashen nahiyar Afirka suka fara gudunar da taro da nufin nazarin gudunmawar da ya kamata kafafen 'yada labarai za su bayar a yunkurin da Duniya ta sa gaba wajen ganin an cimma kudurorin MDD na samar da ci gaba mai dorewa.

Lura da irin rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen aiyukan fadakar da jama’a da dagewarsu akan maganar adalci a sha’anin gudanar da mulki ya sa MDD a shekarun baya nuna bukatar shigar da ‘yan jarida a sabuwar tafiyar da aka sa gaba don ganin an cimma kudirorin ci gaba mai dorewa kafin shekarar 2030.

‘Yan jarida daga kasashen Afirka kimanin 15 ne ke halartar wannan taro na karawa juna sani, kuma a cewar Alain Asogba na jamhuriyar Benin lokaci ya yi da za a dama da ‘yan jarida a kowane fanni na harkokin gudanar da kasa, a maimakon a daukesu a matsayin manema labarai kawai.

Sakataren ofishin Ministan watsa Labarai Abdoulaye Coulibaly da yake jawabin bude taro ya ce yunkurin , ya yi dai dai da abubuwan da gwamnatin Nijar ta sa gaba.

Ga rahoto a sauti daga wakilin Muryar Amurka Souley Mopumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: An Fara Taron Nazarin Gudunmawar 'Yan Jarida Don Cimma Kudurori