Nijar: Mutane 5 Suka Rasa Rayukansu A Wani Harin Ta'adanci

Dakarun Najeriya 'yan bindiga a Jihar Zamfara.

A jamhuriyar Nijar wani harin ta’ddancin da aka kai a kauyen Abare na karkarar Filingue ya yi sanadiyar mutuwar jami’an tsaron jandarma 5, yayin da maharan suka lalata wata mota 1 kafin su gudu da wasu makaman yaki.

Rahotanni daga karkarar Filingue na cewa da yammacin ranar Asabar ne ‘yan bindiga akan Babura suka kai farmaki kan jami’an tsaron bataliyar GARSI da ke aikin sintiri a kewayen kauyen Abare na karamar hukumar Sanam. 'Yan bindigar sun yi amfani da ranar cin kasuwar kauyen na Abare domin sajewa da jama’a lamarin da ya basu damar yin nasara.

Ko da yake rahotanni na cewa an karkashe ‘yan bindiga masu tarin yawa a yayin wannan gumurzu, wata majiya na cewa maharan sun juya zuwa inda suka fito abin da ke nunin bukatar kyautata mu’amula a tsakanin jami’an tsaro da mutanen gari don kawar da dukkan wani tunanin hada kai da ‘yan ta’adda.

Har yanzu ba wata sanarwa a hukunce dangane da wannan hari na kauyen Abare, haka kuma dukkan wani yunkurin jin ta bakin hukumomin tsaro ya ci tura.

Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Mutane 5 Suka Rasa Rayukansu A Wani Harin Ta'adanci