Nijer: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin 'Yan Sanda

'Yan bindiga sun kai hari a garin Komabangou na yankin Tilabery a daren Asabar.

An kwashe kusa sa'a guda ana dauki badadi lokacin da ‘yan bidigar da ba san ko su waye ba, suka kai farmaki a ofishin ‘yan sanda kauyen komabangou dake tazarar kilomita 179 a kudu maso yammacin birnin yamai, lamarin da ya haddasa asarar rayuka a dukkan bangarorin biyu, tare da haddasa asarar dukiyoyi kamar yadda wani mazaunin garin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka.

Gwamnan yankin Tilabery Tijani Ibrahim Katchiela, ya tabbatar da faruwar wannan al’amari sannan ya tabbatar da mutuwar dan sanda guda, wani guda kuma ya sami rauni. An dai kona ofishin ‘yan sandan na komabangou haka kuma an hallaka dan bindiga guda.

Garin Komabangou na gundumar Tera mai makwaftaka da garuruwan iyakar Burkina Faso, ya yi fice ne a wannan yanki kasancewarsa mai mahakar zinaren gargajiya abin da ya sa mutane daga ciki da wajen Nijer ke kwarara don zuwa neman arziki. Koda yake babu wata kungiyar da ta dauki alahkin kai wannan hari, wasu ‘yan kasa na alakanta abin da aiyukan ta’addancin da ake fama da shi a kasashen Mali, Nijer da Burkina Faso.